A jawabin da ya gabatar a zaman taro na duniya domin girmama babban jikan Manzon Allah kuma daya daga cikin shugabannin samarin gidan aljanna Imam Hasan Al-Mujtaba {a.s} a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a jiya Lahadi; Shugaban kasar Iran Sheikh Hasan Ruhani ya yi kira ga hada karfi da karfe a tsakanin kasashen musulmi wajen yaki da ta’addanci, yana mai fayyace cewa; Dole ne mu daga murya tare da hada kai waje guda domin daukan matakan yaki da ta’addanci da masu kafirta musulmi a dukkannin kasashen musulmi.
Sheikh Ruhani ya kuma gargadi kasashen da suke tallafawa ‘yan ta’adda da ayyukan ta’addanci da kudaden man fetur da cewa babu makawa nan kusa kadan zasu fuskanci matsalar ta ta’addanci a cikin kasashensu, inda kaikayi ta koma kan mashekiya.
Har ila yau Shugaban kasar ta Iran ya jaddada wajabcin hadin kan al’ummar musulmin duniya domin fuskantar babban hatsarin da ke tunkararsu, inda masu riya bautan Allah alhalin masu bautar Shaidan ne suke zubar da jinin al’umma da sunan addini a sassa daban daban na kasashen musulmi.